Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-26 10:46:39    
Rundunar injiniya ta kasar Sin ta sauka kasar Sudan domin tabbatar da zaman lafiya a Darfur

cri

Wannan ne rundunar farko ta kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya da ta isa yankin Darfur. Kafin ta tashi daga nan kasar Sin, a gun bikin ban kwana, laftanar kanar Shangguan Linhong wanda ke jagorancin wannan rukunin farko na rundunar aikin injiniya ya ce, "Muhimman nauyin da ke bisa wuyanmu su ne, gina sansanoni da ayyukan yau da kullum domin rundunonin aikin injiniya da majalisar dinkin duniya za ta tura yankin Darfur na Sudan. Sabo da haka, sauran rundunonin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. za su iya shiga yankin Darfur kamar yadda ya kamata bisa shirin da aka tsara."

A watan Afrilu na shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta amince da gayyatar da majalisar dinkin duinya ta yi mata, ta tsai da kudurin tura wata rundunar aikin injiniya zuwa yankin Darfur wadda za ta kunshi hafsoshi da sojoji 315, matsakaicin shekarunsu na haihuwa ya kai 26. Bayan da aka kafa ta a watan Yuni na shekarar da muke ciki, ana ta yi mata horaswa a garin Qingyang na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin. Bayan da wannan rundunar soja ta je kasar Sudan, muhimman nauyin da ke bisa wuyanta su ne, gina filin jirgin sama da shimfida zaman lafiya da gadoji da sansanoni da haka rijiyoyi domin sauran rundunonin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da ke yankin Darfur. "Da farko dai, mun kara mai da hankali kan horar da sojojin da su kiyaye kansu. Yanzu karfin kiyaye kansu da hafsoshi da sojojin rundunar ya samu kyautatuwa sosai. A waje daya kuma, an horar da sojoji ilmin injiniya da kyautata ingancin kayayyaki da makaman da suke cikin hannunsu. Haka kuma, mun kara mai da hankali kan yadda rundunar za ta iya fama da matsaloli da hadarurukan da za su faru a gabansu ba zato ba tsammani. Bugu da kari kuma, an koyar wa sojoji ilmin yau da kullum game da aikin kiyaye zaman lafiya da dai makamatansu."


1 2 3