
A ran 24 ga wata, rundunar aikin injiniya ta kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin ta rukuni na farko ta sauka birnin Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu, ta haka, ta zama runduna ta farko da ke kiyaye zaman lafiya a wannan yanki bisa umurnin Majalisar Dinkin Duniya. A ran 23 ga wata da dare ne wannan rundunar aikin injiniya ta kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin ta rukuni na farko ta tashi daga birnin Zhenzhou na kasar Sin.
"Dukkan sojoji suna nan, sai ku shiga jirgin sama."
Da misalin karfe 9 na dare na ran 23 ga wata, wannan rundunar aikin injiniya ta kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin da ke kunshe da hafsoshi da sojoji 135 sun tashi daga filin jirgin sama na kasa da kasa na Xinzhen na birnin Zhenzhou zuwa kasar Sudan domin aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Durfur na kasar.
1 2 3
|