
Bisa bunkasuwar masana'antu a kasashe daban daban, mutanen da ke zama a garuruwa suna karuwa. A farkon karni na 20, mutanen da ke zama a cikin garuruwa sun dau kashi 5% ne kawai na yawan mutanen duniya, amma ga shi yanzu adadin ya riga ya karu har zuwa 45%, wato ke nan mutane biliyan 2 da miliyan 500 ne na zama a garuruwan duniya. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa shekarar 2025, yawan mutanen duniya da ke zama a cikin garuruwa zai kai kashi 67%. Masana sun yi nuni da cewa, sakamakon sabanin da ke tsakanin saurin karuwar mutane da kuma rashin saurin bunkasuwar garuruwa, za a kara samun cunkuson mutane a biranen duniya a nan gaba.(Lubabatu) 1 2 3
|