Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-16 18:35:29    
Ranar muhallin zama ta duniya

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Asabe Ibrahim, wadda ta fito daga birnin Gusau da ke jihar Zamfara, tarayyar Nijeriya. Malamar ta turo mana wasika a kwanan baya da ke cewa, na ji labarinku cewa, ranar 1 ga wata rana ce ta muhallin zama na duniya, shin mene ne ma'anar ranar, ina so ku ba ni tarihin ranar.

A ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1985, an zartas da wani shiri a gun babban taron MDD na karo na 40, inda aka tsai da ranar Litinin na farko a cikin watan Oktoba na kowace shekara a matsayin ranar muhallin zama na duniya, wato "world Habitat Day", kuma dalilin da ya sa aka yi hakan shi ne don yin kira ga jama'a da su mai da hankulansu a kan muhallin zama na 'yan Adam da kuma hakkin kowa na samun gidajen zama, tare kuma da yin kira ga gwamnatocin kasashe daban daban da su dora muhimmanci a kan gidajen zama da kuma batutuwan da abin ya shafa.

Don fadakar da jama'a a kan muhimmancin kyautata muhallin zama, MDD ta kan tabbatar da wani take kan ranar a kusantowar ranar muhallin zama ta kowace shekara, sa'an nan, ta kan zabi wani birni don a gudanar da bukukuwa. Sa'an nan tun daga shekarar 1989, MDD ta fara samar da lambar yabo ta MDD kan muhallin zama, don nuna yabo ga gwamnatoci da kungiyoyi da kuma mutane masu zaman kansu wadanda suka taka kyakkyawar rawa a wajen kyautata muhallin zama na dan Adam da kuma karfafa musu gwiwa.


1 2 3