Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-16 18:35:29    
Ranar muhallin zama ta duniya

cri

A hakika batun muhallin zama na dan Adam wani batu ne na duk duniya. A farkon shekarar 2007, a karo na farko ne yawan mazaunan garuruwa ya tashi daya da na kauyuka. A cikin 'yan shekarun baya, bisa saurin karuwar mutanen duniya da kuma kwararowar mazaunan kauyuka zuwa garuruwa, muhallin zama na birane ya yi ta lalacewa. Matsaloli iri daban daban sun yi ta karuwa. Bayan haka, rashin tsaro da adalci ya riga ya zama wani babban kalubalen da ke gaban muhallin zama a birane. Bisa kididdigar da MDD ya bayar, an ce, yanzu kusan kashi 32% na mutanen duniya suna zama a cikin garuruwa da birane, kuma mutane kimanin biliyan daya suna zama a cikin unguwannin matalauta. Sa'an nan, a dukan wuraren zama na dan Adam, mutane fiye da biliyan daya suna fama da karancin gidajen zama ko kuma matsalar mugun muhallin zama, kuma a kalla dai mutanen miliyan 100 ba su da gidajen zama, a yayin da mutanen miliyan 600 ne ke zama cikin muhallin da zai iya lalata lafiyar jikinsu.


1 2 3