Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-15 15:41:42    
Har ila yau halin rikicin siyasa da ake ciki a kasar Georgir bai lafa ba tukuna

cri

Daga wani fanni daban kuma, don su kungiyoyi masu yin adawa, ba abu mai sauki ba ne gare su don su samun nasarar babban zaban. Sabo da yanzu kungiyoyi masu yin adawa suna zama a rarrabe a cikin kasar Georgir, ban da manufar "ka da Saakashvili" da "yin adawa da Rasha", kusan a ce ba za su kafa sauran tsare-tsaren siyasa ba, sa'an nan kuma ba su sumu wani babban mutun yin shugabancinsu ba, ballaantana ma cikin shekaru 3 da 'yan watannin da suka wuce, aikace-aikacen da aka yi a kasar sun jawo wa fararen hula karayar zuci.

Amma don su kasashen Amurka da Rasha wadanda suke nada hannunsu suna kallo, wa zai iya kara samun babbar moriya daga cikin wannan hargitsin siyasa na kasar Georgir? Har ila yau ba a iya ba da amsa sosai kan wannan tambaya ba tukuna. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da kungiyoyi masu yin adawa da ke cikin kasar Georgir wadanda ke neman Mr. Saakashvili da ya sauka daga mukaminsa ba "kungiyoyi masu nuna goyon baya ga Rasha" ba, amma shugaban kasa na yanzu da kungiyoyi masu yin adawa dukkansu suna nuna goyon baya ga kasashen yamma, kuma suna yin gaba da juna, wannan ya ba kungiyoyi masu nuna goyon baya ga Rasha damar domawa don sake tafiyar da harkokinsu a kasar. (Umaru)


1 2 3