Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-15 15:41:42    
Har ila yau halin rikicin siyasa da ake ciki a kasar Georgir bai lafa ba tukuna

cri

A ran 14 ga wata, madam Nino Burdzhanadze, shugabar majalisar dokokin kasar Georgir ta ba da jawabi ta rediyo mai hoto inda ta sanar da cewa, daga ran 16 ga wata, za a soke dokar ta baci da ake tafiyar da ita yanzu a cikin kasar. Manazarta sun bayyana cewa, wannan kudurin da hukumar Georgir ta tsayar da matakin da aka dauka na yin zaben shugaban kasar tun kafin lokacin da aka tsayar za zu iya kyautata halin da ake ciki a kasar cikin dan lokaci, amma sabo da ranar yin zaben shugaban kasa ta gabato, kungiyoyin siyasa daban-daban za su kara yin kokawa a tsakaninsu kan matsalar rarraba ikon mulkin kasar, sabo da haka har ila yau halin rikicin siyasa da ake ciki a kasar Georgir bai lafa ba tukuna.

Daga ran 2 ga wata, Kungiyoyi masu yin adawa na Georgir sun fara yin tarurruka a filin da ke bakin kofar babban ginin majalisar dokokin da ke birnin Tbilisi, hedkwatar kasar, inda suka nemi da a yi zaben majalisar, da sauya tsarin shugaban kasa wato tsarin mulkin kasa zai zama tsarin majalisar dokoki, kuma sun nemi shugaban kasa Mr. Mikhalil Saakashvili zai sauka daga mukaminsa.


1 2 3