Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-15 15:41:42    
Har ila yau halin rikicin siyasa da ake ciki a kasar Georgir bai lafa ba tukuna

cri

A hakika kuwa wannan hargitsin siyasa da aka yi cikin kwanaki da yawa ya zama wata babbar barkewar sabani iri-iri da aka yi tun bayan juyin-juya halin da ake kira Rose revolution da aka yi a shekarar 2004 a kasar Georgir. Bayan da Mr. Saakashvili ya ci zaben zama shugaban kasar, ya yi gaggawa don habaka ikon mukaminsa na shugaban kasa ta hanyar gyara tsarin mulkin kasar, amma bai mai da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasar ba. Sabo da haka jama'ar Georgir sun gane cewa, ba za a iya tabbatar da manyan manufofi 3 wato "kawar da al'amuran cin hanci da rashawa, da bunkasa tattalin arziki da kuma maido da cikakkiyar mallakar kasa" da Mr. Saakashvili ya tsayar a farkon lokacin hawa karagar mulkinsa ba.

A lokacin da kungiyoyi masu yin adawa suke neman Mr. Mikhalil Saakashvili zai sauka daga mukaminsa, ya kasa nuna karfin hali wajen yin danniya ga masu yin zanga-zanga, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da idan ya dauki wannan mataki, shi jarumin "juyin-juya halin demokuradiyya" zai sa hular "mai mulkin fira'unanci" a kansa, kuma ba ya son mika mulkinsa ga wani daban, sabo da haka ba yadda zai yi sai ya tsai da kudurin yin zaben shugaban kasa tun kafin lokacin da aka tsayar.


1 2 3