Ban da haka kuma, firaministocin kasashen biyu za su yi shawarwari wajen fadada ganawar da ke tsakanin iyalan da suka rasa juna na kasashen biyu. Yanzu, kasashen biyu suna shirin ganawar iyalan da suka rasa juna sau biyu ko uku a bikin bazara, da bikin haduwar iyali, da ranar samun 'yanci a ran 15 ga watan Agusta a ko wace shekara, amma wannan bai iya cika burin mutanen da suka rasa iyalansu na kasashen biyu. Kasar Korea tana fatan za a yi shiri irin na wannan ganawa a kowane wata, kuma ya kamata a kara yawan mutane daga 100 na kowane bangarorin biyu zuwa 200.
A karshe kuma, firaministocin kasashen biyu za su yi shawarwari wajen kafa yankin hadin gwiwa na kera jirgin ruwa, da shirin gyara hanyoyin motoci da hanyoyin jiragen kasa na kasar Korea ta arewa. 1 2 3
|