Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 16:11:36    
An yi shawarwari tsakanin firaministocin kasashen Korea ta arewa da ta kudu

cri

Ran 14 ga wata a Seoul, babban birnin kasar Korea ta kudu, an fara yin shawarwari tsakanin firaministocin kasashen Korea ta arewa da ta kudu wanda za a shafe kwanaki uku ana yinsa. Mr. Han Duck-Soo firaminista na majaliasr gudanarwar kasar Korea ta kudu da Mr. Kim Yong-il faministan majalisar ministoci na kasar Korea ta arewa sun jaroganci kungiyoyinsu bi da bi sun halarci wadannan taro. Wannan shawarwarin da ake yi su ne shawarwarin tsakanin firaministoci na kasashen biyu bayan shawarwarin koli a karo na 8 da suka yi a shekarar 1992. Bangarorin biyu za su yi shawarwari wajen shirin aiwatar da "sanarwar neman bunkasuwa cikin zaman lafiya tare da bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen Korea ta arewa da kudu" da aka daddale a taron koli a karo na biyu da aka yi a watan Oktoba na shekarar da muke ciki.

A farkon watan Oktoba, shugaba Roh Moo Hyun na kasar Korea ta kudu da shugaba Kim Jong-il na kasar Korea a arewa sun yi shawarwari a Pyangyong, kuma sun bayar sanarwar tarraya, inda suka ce za su daddale yarjejeniyoyi a jere wajen kara yin shawarwarin tsakanin bangarorin biyu, da fadada hadin gwiwa kan tattalin arziki da ayyukan jin kai, da kafa tsarin zaman lafiya na tsibirin Korea da kuma batun rashin nukiliya. Bangarorin biyu sun yi niyyar cewa, a watan Nuwamba, kasashen biyu za su yi shawarwari tsakanin firayin ministocinsu domin sa kaimi ga yunkurin shimfida wannan sanarwar tarraya.

Kafin wannan kuma, firaministocin kasashen biyu sun taba tuntuba da juan har sau uku, kuma sun sami ra'ayoyi iri daya kan wasu batutuwan da ke kunshe da kafa yankin hadin gwiwa na tekun yamma na tsibirin Korea, da warware batutuwan yankin masana'antun da ke Kaesong a fannoni uku, da kuma fadada ganawar da ke tsakanin iyalan da suka rasa da juna.


1 2 3