Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 16:11:36    
An yi shawarwari tsakanin firaministocin kasashen Korea ta arewa da ta kudu

cri
 

Ana ganin cewa, kafa yankin hadin gwiwa na tekun yamma na tsibirin Korea shi ne daya da ke cikin manyan nasarorin da aka samu a cikin taron koli na zagaye na biyu. A cikin wannan shiri, ana fatan kasashen biyu za su bunkasa tekun yamma na tsibirin Korea tare, kuma za a kawar da rikicin soja a haddin teku da ke tsakaninsu.

A cikin wadannan shawarwari, firamistocin kasashen biyu za su yi kokarin warware matsalolin da suke da su a yankin masana'antu na Kaesong a fannonin zirga-zirga, da sadarwa, da kuma kwastan. A watan Yuni na shekarar 2003, kasashen biyu sun fara gina yankin masana'antu na Kaesong, yanzu akwai kamfannoni fiye da 40 na kasar Korea ta kudu suna zaune a wannan yanki, kuma yawan mutanen kasar Korea ta arewa da suke aiki a wadannan yanki ya kai fiye da dubu 17. Haka kuma, yanzu wannan yanki ya riga ya zama alamar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu. Amma saboda akwai kasancewar matsaloli kan fannonin zirga-zirga, da sadarwa, da kuma kwastan, wannan ya kayyade bunkasuwar kamfannonin da ke zauna a wannan yankin masana'antu. Shi ya sa, ana fatan wadannan shawarwarin da ke tsakanin firaministocin kasashen biyu za su warware wannan matsaloli, ta yadda za a kawo wani hali mai kyau ga kamfannonin kasar Korea ta arewa.


1 2 3