Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 15:15:22    
Kada a mayar da mafarin koguna uku na kasar Sin da za su zama tekun da ake kazamtar da shi bisa sakamakon yin amfani da leda

cri

A sa'I daya kuma, sassan da abin ya shafa su ma sun tsara dabaru da manufofi a jere a kan batun.

A cikin 'yan shekarun nan da aka bayar da ka'idojin, aikin kiyaye mafarin koguna uku yana kara samun karbuwa sosai daga wajen mutane a kowace rana, kuma an sami sakamakon farko. Wakilin gidan rediyon kasar Sin ya taba karawa da wani malami Wang da ke sayen kayan abinci a kasuwa , lokacin da ake magana kan matsalar leda, sai Mr Wang ya ce ya fahimci batun hana yin amfani da leda. Ya bayyana cewa,

A wajen kiyaye muhallin halittu, yin amfani da leda zai kawo barna sosai ga muhallin halittu, saboda haka mu kan yi amfani da takardar jarida don kunshi kayan masarufin da muka saya.

Kauyen Batang na garin Jiegu mazauna ne na makiyayya. A da, a ko'ina ana iya ganin leda a makiyayyai, wannan ya kawo barna mai tsanani sosai ga shanu da dawaki da sauran dabbobin da muke kiwonsu, kuma ya kawo barazana mai tsanani ga zaman rayuwarmu makiyayya. Wani mai kiwon dabbobi mai suna Duomaqingmei da ke zama a wurin har fiye da shekaru 60 ya bayyana cewa,

A da, a makiyayyar, a ko'ina ana iya tarar da leda masu launuka iri iri. Da shanu da awaki suke ganinsu, to za su cinye su, amma ba su iya narke da su ba, saboda haka yawancinsu sun mutu bisa sanadiyar cinye leda, na taba kiwon shanu da yawansu ya kai dubu ko fiye, amma yawancinsu sun mutu bisa sakamakon hakan.

Daidaita matsalar da aka samu bisa sakamakon yin amfani da shara mai launin fari ya samar da fa'ida ga makiyaya sosai, wani tsohon makiyayi mai suna Duoma ya yi farin ciki da cewa,

Ina goyon bayan manufar nan da aka tsara, duk saboda ta daidaita wa makiyaya matsala mai wuyar daidaituwa, yanzu, ina kiwon dabbobi cikin kwanciyar hankali sosai.

A lokacin da ake soma daidaita matsalar, sassan da abin ya shafa suna fahimtar da cewa, ya kamata a kara kyautata tunanin makiyayya wajen kiyaye muhallin halittu, game da wannan, hukumar jihar Yushu ta yi kokari sosai wajen ba da tarbiyya ga yara, makarantun wurin suna mai da hankali sosai ga samar wa 'yan makaranta ilmin kiyaye muhallin halittu da shirya sauran ayyuka dangane da yadda za a kiyaye muhallin halittu.(Halima)


1 2 3