Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-14 15:15:22    
Kada a mayar da mafarin koguna uku na kasar Sin da za su zama tekun da ake kazamtar da shi bisa sakamakon yin amfani da leda

cri

A cikin shirinmu na yau da muka shirya muku musamman domin babban taro na 17 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da za a kira a gaba ba da dadewa ba. Yau za mu karanta muku wani bayanin da ke da lakabi haka: Kada a mayar da mafarin koguna uku na kasar Sin don su zama tekun da aka kazamtar da shi bisa sakamakon yin amfani da leda.

Jama'a masu sauraro, lardin Qinghai da ke yammacin kasar Sin ya yi suna sosai a duniya bisa sunansa na cewar wai haikalin ruwa na Asiya. Muhallin abubuwa masu rai da marasa rai da ke kasancewa a yankunan kiyaye halittu da ke kunshe da tabkin Qinghai da Kogin Yangtse da rawayen kogi da mafarin Lancangjiang na cikin lardin ya ba da tasiri kai tsaye ga zaman rayuwar rabin yawan mutanen duniya. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, wakilan gidan rediyon kasar sin sun kai ziyara a lardin Qinghai, kuma sun rubuta bayanai dangane da jituwa da ke tsakanin 'yan adam da halittu.

Jihar kabilar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta yankin Yushu da ke lardin Qinghai tana tsakiyar yankunan kiyaye halittu na mafarin koguna uku bisa matsayin kasar Sin. Bisa matsayinta mai muhimmanci na yin zirga-zirga a kan hanyar da ke hada da jihar Tibet da lardin Sichuan da jihar Xining na kasar Sin, yankin Yushu na da wadatattun makiyaya tare da mutane masu hazikanci da kasa mai ni'ima. A inda, ba a iya ganin bututu masu tsayi sosai na fitar da hayaki, kuma ba a iya saurarar babbar karar da ta fito bisa sanadiyar aiki da injuna, ko'ina ana iya ganin manyan tsaunuka da makiyayai da korama da tabki wadanda ba a iya tsinkayar karshensu ba.

Kawu, kada ka zubar da shara a ko'ina, yin hakan zai kawo barna sosai ga mafarin kogunanmu uku.


1 2 3