Abin da kuke saurara dazun nan shi ne abin da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya ji ya gani a wani titin yankin Yushu . Sharar da wani dan makarantar firamare ya yi magana a kai shi ne leda da mutane suke amfani da su a zaman rayuwar yau da kullum, an kuma kira irin wannan shara da cewar wai shara mai launin fari. Shara mai launin fari shi ne muhimmin abun da ya kawo wa mafarin koguna uku barna wajen kiyaye su. Don daidaita matsalar, a shekarar 2004, jihar Yushu ta kabilar Tibet mai ikon aiwatar da harkokinta na kanta ta soma bayar da ka'idoji dangane da yadda za a hana yin amfani da kayayyakin leda da za a yi amfani da su a cikin karo daya kawai. Ka'dojin sun tsai da cewa, a cikin jihar, kada a yi amfani da kwanon leda na tanadin abinci da da sauran kayayyakin leda da za a yi amfani da su a karo daya kawai, kuma an dora wa kungiyar sa ido kan muhalli nauyin aiwatar da harkokin shari'a da kuma yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka keta ka'idojin. Ka'idojin sun zama na farko da aka bayar a duk fadin kasar Sin .
Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin gine-gine da kiyaye muhalli na gundumar Yushu Mr Ma Chende wanda ke daukar nauyin daidaita matsalar kazamtar da muhalli da aka samu ta hanyar yin amfani da shara mai launin fari ya gaya wa manema labaru cewa, jihar kabilar Tibet mai ikon aiwatar da harkokinta na kanta ta mayar da tattalin arzikinta bisa matsayin mai muhimmanci wanda ayyukan yawon shakatawa ke zama babban jigonsa ta hanyar raya muhallin halittu masu rai da marasa rai , kuma ayyukan gyara kayayyakin gona ke zama kananan sana'o'in ba da taimakon kai. Saboda haka aikin kiyaye tsohon muhallin halittu masu rai da marasa rai ya zama nauyi da ke bisa wuyan yankin Yushu sosai da sosai. Bisa matsayin cibiyar yankunan kiyaye halittu ta mafarin koguna uku, ya kamata yankin Yushu ya ba da misali ga aikin daidaita matsalar da aka samu bisa sakamakon yin amfani da shara mai launin fari. Mr Ma Chende ya bayyana cewa,
Ana kasancewa cikin mawuyacin hali sosai a matakin farko na daidaita matsalar kazamtar da muhallin halittu, kuma ba wanda ya fahimci muhimmancin aikin . An bayyana cewa, a ko'ina a dukkan wurare, ciki har da birnin Xining, hedkwatar lardin da birnin beijing, ana yin amfani da leda, yankin Yushu yana wurin da ke dab da bakin iyakar kasa kuma nesa da bakin teku sosai, amma ana kayyade yin amfani da leda sosai, wannan ya kawo matsaloli da yawa ga jama'ar farar hula wajen zaman rayuwarsu.
A gaban wadannan matsaloli, hukumar kula da gine-gine da kiyaye muhallin halittu ta rattaba hannu kan yarjejenoyoyi a jere tare da wadanda suke sayar da kayayyaki tare da hukumomin kula da aikin yawon shakatawa na jihar da na gunduma don daidaita matsalar da aka samu bisa sakamakon yin amfani da leda . Sa'anan kuma an ba da lacca dangane da kiyaye muhallin halittu a cikin makarantu da hukumomin gwamnati da rundunonin soja. Sa'annan kuma, ta hanyar shirye-shiryen TV na wurin ne, ake gabatar da ilmin kiyaye muhallin halittu ga dimbin jama'ar farar hula ta hanyar yin amfani da harshen Sinanci da harshen Tibet don kara musu fahimtar aikin kiyaye muhallin halittu.
1 2 3
|