Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-06 10:26:46    
Kasashen Sin da Afirka sun bude sabon shafi a fannin yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki

cri

Har kullum gwamnatin Sin na karfafa gwiwa da jagorancin masana'antun kasar Sin iri daban daban masu suna da kuma karfi da su yi hadin gwiwa da kasashen Afirka kan shirye-shiryen injiniya bisa ingantttun fasahohi cikin jimla da fasahohin kula da ayyuka. A gun taron shekara-shekara na Bankin raya Afirka da aka yi a birnin Shanghai na kasar Sin a watan Mayu na wannan shekara, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya jaddada cewa, game da karfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, ya zama wajibi a kara mai da hankali kan ayyukan jin dadin jama'a, musamman ma a kan muhimman ayyukan al'umma da aikin gona da kiwon lafiya da aikin ilmi da rage talauci da kiyaye muhalli, wadanda jama'ar Afirka ke maraba da su. Bugu da kari kuma, malam Wei Jianguo, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya nuna cewa, kyautata aikin gona da aikin kera da sarrafa injuna da sufuri da aikin sadarwa da aikin yin amfani da ruwa da samar da wutar lantarki da sauran muhimman ayyuka su ne muhimman fannonin da kasar Sin ke dora muhimmanci a kai ta fuskar zuba jari.

A halin yanzu, kasashen Sin da Afirka sun shiga sabon mataki wajen yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki, wato suna yin hadin gwiwa a fannoni daban daban cikin da'irori daban daban. Tabbas ne bangarorin 2 za su samar da kyakkyawar makoma a fannin raya huldar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu, bisa tushen zumuncin gargajiya a tsakaninsu da kuma tsayawa kan hakikanan ra'ayi bisa halin da ake ciki da tunanin kirkire-kirkire.(Tasallah)


1 2 3