Kasashen Sin da Afirka aminai ne suka hada gwiwa da kuma taimakawa juna bisa matsayin rinjaye da moriyar juna da kuma neman samun nasara tare. Bayan da suka shiga sabon karni, bangarorin 2 sun sami saurin yalwatuwar cudanyar tattalin arziki da ciniki, musamman ma bayan da suka sami nasarar kiran taron koli a Beijing na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2006, wato suka bude sabon shafi daban a fannin ingantuwar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki.
A farkon rabin wannan shekara kawai, jimlar kudaden da kasashen Sin da Afirka suka samu daga wajen yin ciniki a tsakaninsu ta kai misalin dalar Amurka biliyan 32, wadda ta karu da rubu'i bisa na makamancin lokaci a shekarar bara. Kasar Sin na matsayi na uku ga Afirka a fannin yin ciniki.
Kyakkyawar bunkasuwar ciniki a tsakanin Sin da Afirka na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikinsu duka da kuma kyautata zaman rayuwar jama'arsu duka. Kayayyakin kasar Sin masu inganci da araha na cancanta matsayin saye-saye na kasuwannin Afirka sosai, sun kuma biya bukatun jama'ar Afirka, shi ya sa suka sami matukar yabo daga masu saye-saye na Afirka.
Afirka na daya daga cikin yankunan da masana'antun kasar Sin suka fi son zuba kudi a kai. A cikin farkon rabin wannan shekara, masana'antun kasar Sin sun riga sun zuba dalar Amurka misalin milyian 480 kan Afirka kai tsaye, yawan kudaden ya karu sosai bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.
1 2 3
|