Shirye-shiryen da kasar Sin ke zuba kudi a kai na cikin kasashe 49 na Afirka, wadanda suka shafi ciniki da kera da kuma sarrafa kayayyaki da sarrafa albarkatu da sufuri da aikin gona da inganta amfanin gona daga dukkan fannoni. Zuba jari da kasar Sin ke yi wa Afirka ya sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da kuma samar da karin guraban aikin yi a wurin da kawo wa kasashen Afirka fasahohin da ke dacewa da su da kuma inganta karfin kasashen Afirka a fannin bunkasa kansu, shi ya sa ya sami karbuwa sosai a Afirka.
Daddale kwangila tare da kamfanonin waje kan ayyukan yau da kullum wani abu ne daban da ya fi jawo hankali a fannin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Masana'antun kasar Sin sun habaka shirye-shiryensu sannu a hankali bisa kyakkyawar huldar siyasa a tsakanin Sin da Afirka da kuma gine-gine masu inganci da araha, sun kuma yi ciniki a kasuwannin ba da kwangila kan ayyukan yau da kullum na Afirka. A sakamakon shiga muhimman ayyukan kasashen Afirka, masana'antun kasar Sin ba kawai sun samar da gine-gine masu inganci ba, har ma sun rage kudaden ginawa, sun kuma daukaka ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma na wurin, shi ya sa suka sami matukar yabo daga gwamnatocin Afirka da jama'arsu.
1 2 3
|