Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-01 15:10:43    
Kotun kasar Spain ta yanke hukunci kan matsalar fashewar bamabamai ta "ran 11 ga Maris" a birnin Madrid

cri

Bisa abubuwan da aka tanada cikin dokokin shari'a na kasar Spain an ce, babu hukuncin kisa da daurin rai da rai a kasar, kome laifuffukan da aka yi za a yanke su ne da hukuncin dauri na wani tsaron lokaci. Amma hukuncin dauri mafi tsawon lokaci da aka yanke kan mafu laifin yin ta'addanci shekaru 40 ne, sabo da haka aka yanke hukunci kan muhimman masu laifuffuka 3 cikin matsalar fashewar bamabamai na Madrid bisa tsarin shari'ar da aka tanada cewa, sun yi laifuffuka da yawa, kuma jimlar tsawon lokacin da aka lissafta bisa hukuncin daurin da aka yanke musu.

A gun taron manema labarun da aka shirya bayan hukuncin dauri da aka shelanta, Mr. Rodriguez Zapatero, firayim ministan kasar Spain ya yi jawabi inda ya yi kyakkyawan yabo cewa, an yanke hukunci kan wannan matsalar fashewar bamabamai na Madrid da sauri, a fili kuma da amfani sosai, kuma ya amince cewa dokokin shari'a suna da adalci. Ya ce, hukuncin da aka yanke kan wannan matsala ya bayyana takanaiman magana na wannan hargitsin fashewar bamabamai, kuma ya nuna adalci ga mutane ta yadda aka debe kewa ga 'yan iyalai masu shan wahala, kuma aka tabbatar da halaccin iko ga 'yan kasar Spain. Kafofin watsa labaru na kasar Spain ciki har da tashoshin internet na rediyo da na telebijin da na jaridu dukkansu sun watsa labarin yanke hukunci kai tsaye, masu karanta shafuffukan internet na jaridar da ta fi buzuwa a kasar Spain sun rubuta sharhohi da yawa cikin shafuffukan internet na wannan jarida, mutane da yawa sun nuna goyon bayansu ga wannan hukuncin da kotun ya yanke, sun ce hukuncin da aka yanke ya faranta ran mutane kwarai da gaske, kuma sun sha nuna goyon bayansu ga gwamnatin kasar da kuma kasashen duniya bisa farmaki mai tsanani da suka tayar kan masu laifuffukan ta'addanci. (Umaru)


1 2 3