Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-01 15:10:43    
Kotun kasar Spain ta yanke hukunci kan matsalar fashewar bamabamai ta "ran 11 ga Maris" a birnin Madrid

cri

Kundin hukunci yana hade da abubuwa kamar haka, an tabbatar da cewa, mutane 2 na kasar Morocco su ne 'yan ta'adda da suka kai wannan harin ta'addanci, wadanda kuma aka yanke musu hukuncin dauri na shekaru 42,924 da shekaru 42,922 bi da bi. Wani mahaki na Spain wanda ya samar wa 'yan ta'adda albarushi a lokacin wanda aka yanke masa hukuncin dauri na shekaru 38,976.

A ran 11 ga watan Maris na shekarar 2004 da safe, yayin da jiragen kasa guda 4 da ke cike da fasinjoji suka shiga cikin birnin Madrid, hedkwatar kasar spain daga karkarar birnin sun fashe bi da bi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 192, yayin da mutane fiye da 1,500 suka ji rauni. Kungiyar 'yan ta'adda ce ta haddasa wannan ta'asa, sabo da haka mutanen Spain suna kiran wannan hargitsi da sunan "Hargitsin 11 ga Satumba na kasar Spain", kuma ya zama hargitsi kai hari mafi mugunta da 'yan ta'adda suka haddasa cikin tarihin kasar Spain.


1 2 3