A ran 31 ga watan Oktoba, kotun kasar Spain ta yanke kukunci kan matsalar fashewar bamabamai da aka yi a ran 11 ga watan Maris na shekarar 2004 cikin jirgin kasa na birnin Madrid, wato an yanke wa muhimman masu laifuffuka 3 dauri na daga shekaru fiye da 30,000 zuwa shekaru 40,000, wannan hukunci da aka yanke ya jawo martani sosai daga wajen sassa daban-daban na kasar Spain.
Daga wajen karfe 8 na wannan rana da safe, manyan akalai guda 3 ciki har da shugaban kotun kasar Spain sun fara dudduba kuma sun sa hannu cikin nitsuwa kan kundin hukunci wanda tsayinsa ya kai shafuffuka 600 kan ubannin laifi 21 da aka tuhume su da laifin fashewar bamabamai da aka yi a ran 11 ga Maris cikin jiragen kasa na Madrid. Bayan sa'o'i 4 wato wajen karfe 12 da minti 30 na tsakar rana, Mr. Gomez Bernudez, shugaban kotun kasar ya karanta kundin hukunci a gaban dubban iyalan masu shan wahala da manema labaru da ke cikin kotun da kuma waje da shi.
1 2 3
|