Daga baya kuma manazarta sun ajiye wadannan beraye cikin wani dakin da ke da fitilu na UVB , kuma sun gano cewa, lallatattun kwayoyin beraye na DNA nasu sun mutu bisa mataki daban daban. Dalilin da ya sanya mutuwar kwayoyi shi ne sabo da kwayoyin sun kashe kansu domin kiyaye lafiyar jiki.
Kuma manazarta sun nuna cewa, idan kwayoyin da suka ji raunuka sakamakon hasken rana suka kashe kansu, to ba za su zama kwayoyin sankara ba. A cikin binciken da aka yi, an gano cewa, idan an kwatanta da beraye na rukunin da ya zama ma'aunin bincike, yawan kwayoyin da suka mutu na rukuni na farko ya yi yawa har ya karu da kashi 95 cikin dari, kuma wannan jimla ta karu da 120 cikin dari ga rukuni na biyu, haka kuma jimlar ta karu kusan kashi 400 cikin dari ga rukuni na uku.
Manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa motsa jiki da kuma shan abinsha da ke kunshe da sinadarin caffein suke iya yin rigakafi kan sankarar fata ba, shi ya sa ake bukatar ci gaba da yin nazari. (Kande) 1 2 3
|