![]( /mmsource/images/2007/10/31/motsa02.jpg)
Manazarta na jami'ar Rutgers ta jihar New Jersey ta kasar Amurka sun bayar da rahoto a cikin jaridar kwalejin ilmin kimiyya na kasar, cewa wani irin sinadarin ultraviolet da ke cikin hasken rana wanda ake kiransa UVB muhimmin sanadi ne wajen haifar da sankarar fata. Irin wannan sinadarin ultraviolet zai iya lalata DNA da ke cikin kwayoyin jikin dan Adam, ta haka za su zama munanan kwayoyi wajen haddasa sankara. Ban da wannan kuma binciken ya gano cewa, watakila motsa jiki da kuma shan abinsha da ke kunshe da sinadarin caffein kamar yadda ya kamata za su iya ba da taimako wajen kashe wadannan munanan kwayoyi.
Manazarta sun zabi beraye da ba su da gashi domin yin musu gwaji, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da idan ba su da gashi, to fatunsu za su fi saukin jin raunuka sakamakon hasken rana. An kasa wadannan beraye cikin rukunoni hudu. Beraye na rukunin farko sun shan ruwan da ke kunshe da sinadarin caffein, wanda yawansa ya yi daidai da kofi na kwafi guda ko biyu da dan Adam yake sha a ko wace rana. Beraye na rukuni na biyu sun motsa jiki a cikin kejin da ke aka iya jure shi. Beraye na rukuni na uku kuwa sun sha ruwan da ke kunshe da sinadarin caffein da kuma motsa jiki, na rukuni na hutu ba su yi kome ba.
1 2 3
|