Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-31 15:47:22    
Ayyukan raya al'adu a kauyuka sun samar wa manoma fa'ida a hakika

cri

Ban da aika wa manoma littattafai , ma'aikatar noma da ta kimiyya da fasha da ta kiwon lafiya da sauransu su ma sun tura kwararrunsu zuwa kauyuka don fadakar da manoma ilmi iri iri.

Kara mai da hankali ga kula da girman samari da kuma kyautata muhallin al'adu da suke ciki aiki ne da wasu sassan da abin ya shafa suke yi a cikin 'yan shekarun nan da suke ciki.

A cikin 'yan shekarun nan goma da suka wuce, an kara fahimtar juna a tsakanin yaran birane da kauyuka, da kuma tsakanin yaran kabilar Han da na kananan kabilu da tsakanin yara masu koshin lafiya da na nakasassu. Mataimakiyar babbar edita ta madaba'ar yara ta kasar Sin malama Lu Qing ta bayyana cewa, a yau da wasu shekarun da suka wuce, an shirya aikin ba da taimakon juna a tsakanin yaran birane da na kauyuka kafada da kafada, amma a cikin 'yan shekarun nan biyu da suka wuce, an kara wasu abubuwa a ciki, wato a kara ba da taimakon juna da yaran manoma kwadago da ke aiki a birane.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da aikin kafa sabbin kauyuka masu tsarin mulkin gurguzu, a cikin aikin, an mayar da aikin al'adu bisa matsayi mai muhimmanci, don a bari manoman duk kasar Sin su iya more sakamakon da aka samu wajen raya al'adu.(Halima)


1 2 3