Tun daga karnin da ya shige, sassa da yawa na gwamnatin kasar Sin suka soma yin hadin guiwarsu wajen aika littattafai ga manoman da suke zama a wuraren da ke iyakar kasa da sauran wuraren da ke nisa da bakin teku na kasar Sin don taimaka musu wajen neman wadata ta hanyar yin amfani da ilmi da fasahohi. A sa'I daya kuma, ta hanyar ayyukan kulla huldar abokantaka a tsakanin samari da sauransu, kungiyoyin jama'a su ma suna sa kaimi ga raya ayyukan al'adu a kauyuka.
A kasar Sin, sassan gwamnati da kungiyoyin jama'a da yawa suna yin ayyuka da yawa don taimaka wa kauyuka wajen kafa manyan ayyukan al'adu don kara daga matsayin manoma wajen al'adu ta yadda za su rike ilmin kimiyya da fasaha sosai da kyautata zaman rayuwarsu a fannin kayayyaki da al'adu. Kwamitin ba da taimako ga matalauta wajen al'adu na kasar Sin wanda aka kafa shi a shekarar 1993 shi ne kungiyar jama'a da ke ba da taimako ga jama'a, dukkan ma'aikatanta suna samar da hidima ga manoma bisa aikin sa kai a lokacinsu na hutu. Sun tattara albarkatan zamantakewar al'umma don ba da taimako ga manoman da ke zama a wuraren da ke iyakar kasa kuma nisa da bakin teku wajen yin amfani da ilmin kimiyya don kubutar da kansu daga halin da suke ciki na fama da talauci, sa'anan kuma ta ba da shawarar kafa muhallin nuna kauna ga sauran mutane da taimaka musu a zamantakewar al'umma. A shekarar 1994, kwamitin da babbar hukumar kula da ayyukan watsa labaru da da'bi ta kasar Sin sun shirya aikace-aikace na kafa dakunan ajiye littattafai a dubban kauyuka, sun kuma gayyaci madaba'a da kantunan sayar da littattafai da jama'ar farar hula don samar wa manoma littattafai a kyauta da kuma kafa dakunan musamman na ajiye littattafai. A cikin 'yan shekarun nan fiye da goma da suka wuce, an riga an kafa irin wadannan dakuna da yawansu ya kai dubu 90 a duk fadin kasar Sin.
Wani manomi mai suna Zhao Wenping ya bayyana cewa, a cikin dakin karatu, ya karanta littattafai da yawa dangane da kimiyya da fasaha, kuma ya yi amfani da wadannan ilmi wajen dasa bishiyoyin ba da 'ya'yan ci, shi ya sa yawan 'ya'yan itatuwan da ya samu ya kara karuwa .ya bayyana cewa, ta hanyar ba da taimako ga matalauta a fannin al'adu da kuma samar wa kauyuka kimiyya da fasaha, mun riga mun sami ilmi a fannoni da yawa, yawan 'ya'yan itatuwan da muka samu ya kara karuwa.
1 2 3
|