Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-31 15:47:22    
Ayyukan raya al'adu a kauyuka sun samar wa manoma fa'ida a hakika

cri

Aikin samar wa manoma littattafai a kyauta ya horar da manoman kasar Sin wajen yin karatu da koyo tamkar ayyukan da suke saba yi kullum, manoma da yawa sun sami wadatuwa kuma sun kubutar da kansu daga halin da suke ciki na fama da talauci . Wasu manoma sun rubuta abubuwa da suka samu a lokacin da suke karatu, kuma sun bayar da bayanansu ta rediyo da jaridu. Kwamitin ba da taimako ga matalauta ya kuma buga litatttafan da ke kunshe da bayanan manoma don samar da sauki ga manoma wajen musanya ra'ayoyinsu dangane da karatu.

Aikin samar wa dubban kauyuka litattattafai a kyauta ya sami sakamako mai kyau sosai, kuma aikin ya jawo hankalin sassan gwamnati sosai da sosai. A shekarar 2006, babbar hukumar kula da aikin watsa labaru da da'bi ta kasar Sin ta soma aikin kafa dakunan littttafai na manoma, kuma ta yi shirin kafa dakunan littattafai da yawansu ya kai dubu 200 a kauyukan kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa, a kowane dakin, za a ajiye littattafai da yawansu ya kai wajen dubu tare da jaridu da mujjalu iri iri da yawansu ya wuce goma da kasaet kaset iri iri fiye da dari, wani shugaba na hukumar mai suna Fan Weiping ya bayyana cewa, littattafan da muka aika wa kauyuka dukansu suna dacewa da bukatun manoma, da manoma suke karatu, sai suka iya yin amfani da ilmin da suka samu daga wajen karatu tare da samun sakamako mai kyau.


1 2 3