Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-31 09:45:15    
Sha'anin wasannin motsa jiki na jama'a ya sami kyakkyawan ci gaba a kasar Sin

cri

Bugu da kari kuma, saboda yawancin mutanen Sin na zama a yankunan karkara, shi ya sa hukumomin kasar Sin a matakai daban daban su ma sun mai da hankulansu sosai kan gudanar da harkokin wasanni a kauyuka. A shekaru 5 da suka wuce, a karkashin shuagabancin kwamitocin harkokin mazauna karkara da hukumomin jama'a na gundumomi da garuruwa da kuma kananan hadaddun kungiyoyin wasanni na manoma, ana tsayawa tsayin daka kan hada wasannin motsa jiki na kauyuka da ayyukan noma da harkokin al'adu tare, sa'an nan kuma, ana gudanar da harkokin wasanni masu ban sha'awa a bukukuwan gargajiya da kuma lokacin da manoma ba su da aiki da yawa. Malam Feng ya kara da cewa,'Ga misali, a shekarar 2006, hukumar jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta shirya gasar wasan kwallon kwando a kauyuka dubu goma, inda kauyuka fiye da dubu 11 suka kafa kungiyoyinsu domin shiga gasar. Sa'an nan kuma, hukumar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta fara yada wasan kwallon kwando a yankunan karkara, ta haka, dukkan kauyukan jihar suna da filayen motsa jiki. Wadannan harkokin wasanni da manoma ke lakanta ba kawai sun inganta zamansu na al'adu a lokacin hutu ba, har ma sun kyautata tunaninsu na motsa jiki, bugu da kari kuma, sun daukaka ci gaban wasannin motsa jiki a karkara.'

Dadin dadawa kuma, a shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta share fagen taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 cikin himma. Hukumomin harkokin wasanni na kasar Sin sun yi amfani da wannan kyakkyawar dama domin shirya harkar 'motsa jikunan dukkan al'umma domin wasan Olympic', ta haka, jama'ar Sin ba kawai sun nuna sha'awa da goyon baya ga taron wasannin Olympic ba, har ma suna himmantuwa kan motsa jiki.

A sakamakon kokari na tsawon shekaru da yawa, yanzu tunanin wasannin motsa jiki na jama'a ya shiga zukatan mutane a kasar Sin, ya kuma ba da babban tasiri kan zaman rayuwarsu. Motsa jiki na matsayin muhimmin aiki ne a fannonin kyautata ingancin jiki da lafiyar mutane da kuma kafa kyakkyawar hanyar zaman rayuwa. (Tasallah)


1 2 3