Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-31 09:45:15    
Sha'anin wasannin motsa jiki na jama'a ya sami kyakkyawan ci gaba a kasar Sin

cri

A shekaru 5 da suka wuce, hukumomin kasar Sin a matakai daban daban sun yi dimbin ayyuka domin kafa tsarin ba da hidimar wasanni ga dukkan al'umma, wanda ke bayyana sigar musamman ta kasar Sin. Sun yi amfani da kudin jin dadin jama'a da suka samu daga yin tanbola domin wasanni, sun gina filayen motsa jiki da na'urorin motsa jiki a unguwannin birane da yankunan karkara da manyan filaye da wuraren yawon shakatawa da kananan wuraren yawon shakatawa da ke tituna da sauran wurare.

Malama Fu Xingxia, wata mazauniyar Beijing, a ko wace rana ta kan je filin motsa jiki da ke cikin unguwarta domin motsa jiki. Ta ce,'Samar da na'urorin motsa jiki a unguwarmu na ba mu sauki sosai, musamman ma tsofaffi. Su kan motsa jiki, su kan yi wasa da wadannan na'urori. Yara kuwa su kan yi wasa da kwallo a ranar Lahadi. Mun fi samun sauki a yanzu. Wadannan na'urori na dacewa da motsa jiki daga dukkan fannoni, kamar su kugu da kafa da hannu. A da mun je wurin yawon shakatawa domin motsa jiki, amma yanzu muna motsa jiki a unguwarmu.'

A shekaru 5 da suka gabata, har kullum hukumomin kula da harkokin wasanni a matakai daban daban na kasar Sin sun fi dora muhimmanci kan gudanar da wasannin motsa jiki a unguwannin mazauna. A halin yanzu, wasannin motsa jiki na samun saurin ci gaba a birane, musamman ma a unguwannin mazauna, haka kuma, mazauna birane suna kara nuna sha'awa kan motsa jiki da sassafe da dare da kuma shiga sauran wasannin motsa jiki sannu a hankali.


1 2 3