Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-31 09:45:15    
Sha'anin wasannin motsa jiki na jama'a ya sami kyakkyawan ci gaba a kasar Sin

cri

A shekaru 5 da suka wuce, sha'anin wasannin motsa jiki na jama'a ya sami babban ci gaba a kasar Sin. Miliyoyin fararen hula na kasar Sin suna cin gajiyar wannan sha'ani.

A shekarar 2002, gwamnatin Sin ta gabatar da cewa, ya zama wajibi a tabbatar da ganin an raya sha'anin wasannin motsa jiki na jama'a da kuma tattalin arzikin al'umma da sha'anin zaman al'ummar kasa tare yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, a shekarar 2020, kasar Sin za ta kafa tsarin ba da hidimar wasanni ga dukkan al'umma, wanda ke bayyana sigar musamman ta kasar Sin.

Lokacin da ya zanta da wakilinmu a kwanan baya, Feng Jianzhong, mataimakin shugaban hukumar harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin, ya yi karin bayanin cewa,'A shekarar 1995, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta gabatar da 'tsarin ka'idoji kan shirin wasannin motsa jiki na jama'a', inda ta tsara shiri da kuma rarraba ayyuka kan raya sha'anin wasannin motsa jiki na jama'ar Sin. A shekarun baya, a lokacin da ake aiwatar da wannan tsarin ka'idoji, hukumomin wurare daban daban na kasar Sin sun mayar da gudanar da wasannin motsa jiki na jama'a ta hanyoyi daban daban a matsayin babban bangare da kuma muhimmiyar hanya ta raya aikin wasannin motsa jiki na jama'a.'


1 2 3