Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:35:50    
Shiyyar Enshi ta kasar Sin tana yada fasahar yin amfani da iskar gas

cri

Bisa labarin da muka samu, an ce, sabo da fasahar yin amfani da iskar gas da shiyyar Enshi take yaduwa yanzu, yawan bishiyoyin da aka rage sarewa a ko wace shekara ya kai kadada fiye da dubu 100, haka kuma yawan filin gandun daji na shiyyar ya kai kashi 67 cikin dari na duk fadin shiyyar, muhallin halittu ya samu kyautatuwa a bayyane. Yaduwar wuraren samar da iskar gas ya canja tsohuwar al'adar wannan shiyyar da ke fama da talauci a kan duwatsu, wato samun makamashi ta hanyar sassare itatuwa, ban da wannan kuma yawan ribar da ake samu kai tsaye wajen yin amfani da iskar gas ya zarce kudin Sin wato Yuann miliyan 150, haka kuma yin amfani da irin ruwa da kuma barbashin abubuwa da aka samu daga iskar gas na iya rage kudaden da aka kashe wajen sayen magungunan kashe wari da kuma takin zamani. Xiao Hongjun, wani manomi na kauyen Denglongba na shiyyar Enshi ya gaya mana cewa,

"ta yin amfani da ruwan banza da dusar iskar gas, an rage yawan maganin kashe kwari da takin zamani da a kan yin amfani da su, kuma amfanin gona da aka samar sun fi tsabta, har sun kai ma'aunin da kungiyar tarayyar Tuwai ta tsara wajen binciken amfanin gona, ta haka an rage yawan kudaden da manoma suka kebe wajen samar da abinci, kuma ribar da suke samu wajen tattalin arziki ta samu karuwa a bayyane."

Tan Shuanghe, shugaban hukumar makamashin halittu ta shiyyar Enshi ya gaya wa wakilinmu cewa, sabo da fasahar yin amfani da iskar gas ta kawo musu ribar tattalin arziki da ta zaman al'umma sosai, shi ya sa suna cikin shirin ci gaba da yada fasahar a nan gaba. Kuma ya kara da cewa,

"yin amfani da wuraren samar da iskar gas ba kawai yana iya sa kaimi ga ayyukan kiwon dabbobi da dasa bishiyoyi ba, har ma ya iya inganta bunkasuwar sana'ar musamman ta shiyyarmu. Kafin shekara ta 2003, ana iya samun abincin hallitu iri 10 kawai a shiyyar, amma a shekarar nan da muke ciki, jimlar ta kai 105. Kuma muna da wani shiri, wato kafin shekara ta 2014, dukkan amfanin gona da shiyyarmu ta samar za su iya biyan bukatun da aka yi wa abincin halittu."(Kande Gao)


1 2 3