Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-30 15:35:50    
Shiyyar Enshi ta kasar Sin tana yada fasahar yin amfani da iskar gas

cri

A shekara ta 2000, a shiyyar Enshi ta kabilun Tujia da Miao ta lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin, an fara dukufa kan bunkasa aikin raya garuruwa da ke da tsabtataccen muhalli ta hanyar yin amfani da iskar gas, ta yadda za a iya kiyaye muhallin halittu da kuma kyautata zaman rayuwar mazaunan wurin. To a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan yadda shiyyar Enshi ke yin amfani da iskar gas.

A da, a kauyuka na shiyyar Enshi, a kan ga dimbin hayaki yayin da ake dafa abinci, a kan shaki iska mai wari daga masai, kuma a kan ga gurbataccen ruwa da kudaje da kuma sauro a ko ina. Irin wannan mumunen muhalli ya yi illa sosai ga lafiyar al'ummar wadannan kauyuka, ban da wannan kuma ana lalata muhallin halittu sosai ta hanyar kona itatuwa masu dimbin yawa domin yin amfani da su a matsayin makamashi a ko wace shekara.

Sabo da haka, gwamnatin shiyyar Enshi ta tsara wani shiri na gina wurare dubu 700 na samar da iskar gas, da kuma samar da kudin taimako daga yuan 500 zuwa 1000 ga kauyawan da suka gina wuraren samar da iskar gas, ta haka yawan wuraren samar da iskar gas ya samu karuwa sosai. Kuma an labarta cewa, ya zuwa yanzu an riga an kammala rabin tsarin.


1 2 3