Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-29 14:20:56    
Tafkin Qinghai wurin zama ne ga bil adama da tsuntsaye gaba daya

cri

Yanzu, hukumar kula da harkokin yankin da ake bayar da kariya ga yanayin kasa ta lardin Qinghai ta riga ta dauki matakai masu yawa don hana dan adam su kawo tasiri ga wurin tafkin'Qinghai' da tsuntsaye ke zama. Alal misali, tsibirin tsuntsayen muhimmin wuri ne ga yankin da ake bayar da kariya ga yanayin kasa a tafkin 'Qinghai'. Ko da yake an amince da masu yawon shakatawa da su kai ziyara a tsibirin, amma duk da haka an shimfida sharudda a kan abubuwa da tilas ne masu yawon shakatawa su kula da su sosai.

Bayan da masu yawon shakatawa suka sauka a tsibirin tsuntsayen, wajibi ne, su shiga cikin motoci masu aiki da wutar lantarki, suna tafiya kan hanyoyi da aka tsaida. Sai a bakin tafkin, masu yawon shakatawa su hango tsuntsaye da madubi mai kawo nesa kusa.

Malam He Yubang, mataimakin shugaban hukumar kula da yankin da ake bayar da kariya ga yanayin kasa na tafkin 'Qinghai' ya bayyana cewa, "ya kamata, ya kasance akwai tazara a tsakanin tsuntsaye da bil-adama. Idan mutane sun tsaya a tsakiyar tsuntsaye, to, ba za a sami zaman jituwa a tsakanin bil-adama da halitta ba. A hakika dai, wannan ya zama babbar wahala ce ga tsuntsaye."

Don rage wahalhalun da bil adama ke kawo wa tsuntsaye masu hayayyafa, an gina wani daki a karkashin kasa ta yadda masu yawon shakatawa su gane wa idanunsu tsuntsaye ta tagogi a wani wuri da ake kira 'tsibirin kwai', Makasudin yin haka shi ne domin yadda mutane ke iya ganin tsuntsaye, amma tsuntsaye ba su iya ganin mutane ba.

Ko da yake masu yawon shakatawa ba su ji dadin da bin irin wannan hanyar kallon tsutsaye ba, amma duk da haka hanyar ta sami fahimta da goyon baya daga wajen yawancin masu yawon shakatawa. Malam Li Shehui wanda ya zo daga birnin Xi'an da ke a arewa maso yammacin kasar Sin ya ce, "ana bin hanyar nan domin kada a haifar da matsaloli ga zaman rayuwar tsuntsaye, ta yadda za su yi hayayyafa yadda ya kamata. Mun iya fahimtar wannan, kuma ina ganin cewa hanyar tana da kyau, kuma ta cancanci a nuna mata yabo. "(Halilu)


1 2 3 4