Lardin Qinghai da ke a yammacin kasar Sin ya shahara a duniya bisa matsayinsa na "tankin ruwa a Asiya". Halin da ake ciki game da yanayin kasa a yankunan da ake bayar da kariya ga yanayin kasa na tafkin Qinghai na lardin da mafarin kogin Yangtse da rawayen kogi da kogin Lancang yana haifar da tasiri ga zaman rayuwar rabin yawan mutanen duk duniya kai tsaye. A cikin shekarun nan da suka wuce, hukumomin matakai daban daban na kasar Sin da jama'arta sun yi amfani da dimbin 'yan kwadago da kayayyaki wajen kyautata muhallin wadannan wurare da kiyaye shi, ta haka a zahiri aka kyautata yanayin kasa na lardin Qinghai.
A yanayin bazara na ko wace shekara, tsuntsaye iri iri har sama da goma su kan yi dogon balaguro daga kudancin kasar Sin da wuraren kudu maso gabashin Asiya zuwa tafkin 'Qinghai' na lardin Qinghai da ke a yammacin kasar Sin. A wannan lokaci, sai tafkin nan mafi kyaun gani a kasar Sin ya zama duniyar tsuntsaye, tsibiri a tsakiyar tafkin inda tsuntsaye ke taruwa ya zama wurin zama ga tsuntsaye da dan adam gaba daya.
1 2 3 4
|