Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-29 14:20:56    
Tafkin Qinghai wurin zama ne ga bil adama da tsuntsaye gaba daya

cri

Daga binciken da aka yi, an gano cewa, matsakaicin yawan tsuntsaye masu kaura da ke zama a tsibirin ya wuce dubu 50 a ko wace shekara. A sakamakon zuwa dimbin tsuntsaye masu kaura, tsibirin 'Qinghai' yana kara shahara a duniya sannu a hankali, ya zama shahararen wurin da masu yawon shakatawa ke zuwa don more idanunsu da tsuntsaye. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, matsakaicin yawan masu yawon shakatawa da ke zuwa tsibirn 'Qinghai' ya kan kai dubu 100 a ko wace shekara.

A tsibirin, wakilanmu sun tarar da Malam Li Shehui na birnin Xi'an da ke a arewa maso yammacin kasar Sin tare da matarsa da kuma diyarsa wadanda ke yawon shakatawa. A karo na farko, diyar ta ga tsuntsaye da yawa kamar haka, ta yi mamaki kwarai. Malam Li ya yi hira da wakilanmu cewa, "mun zo tsibirin tsuntsayen nan ne, musamman domin diyarmu ta ganam ma idonta da tsuntsaye. Na gaya mata cewa, wadannan tsuntsaye sun dade suna zama a nan, idan dan adam su kiyaye muhalli da kyau, to, za su kiyaye tsuntsaye da kyau, tsuntsayen suna zama rayuwarsu ne cikin dogara da dan adam."

Amma tafkin 'Qinghai' wuri ne da sauye-sauyen yanayin duk duniya ke kawo masa tasiri. Don haka yayin da ake bunkasa harkokin yawon shakatawa a wurin, wajibi ne, a yi la'akari da batun kiyaye lafiyar yanayin kasar sosai.

Malam Xu Hao, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta lardin Qinghai ya bayyana a fili cewa, ko kusa bai kamata dan adam su bunkasa harkokin yawon shakataba tare da gurbata muhalli ba. Ya kara da cewa, "mun fahimci cewa, wajibi ne, mu dogara da lafiyar yanayin kasa wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa yadda ya kamata. Tafkin 'Qinghai' ni'imataccen wuri ne da ba safai a kan samu irinsa ba a duniya. Ko kusa ba za mu gurbata shi ba. Sa'anan a daya bangare, idan an gurbata shi, to, sakamako zai kasance mai muni. In haka ya faru, to 'yaya jama'a za su yi zaman rayuwarsu, balle ma tsuntsaye. "


1 2 3 4