Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 13:49:47    
Kasar Sin ba ta samun batun bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima

cri

Daga baya Mr. Zhu ya tabo magana kan sabuwar kididdigar da aka yi a game da CPI wato yawan farashin abubuwan da mazauna birane ke saya. Ya bayyna cewa: " Idan an duba halin da ake ciki yanzu a kasar Sin, to ana ganin cewa, yawan CPI na kasar daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar da muke ciki ya karu da kashi 4.1 cikin kashi 100, wato ke nan an samu karin kashi 0.2 cikin 100 bisa na watan Agusta na wannan shekara".

Bugu da kari, Mr. Zhu Zhixin ya karyata labari cewa wai an samu raguwar darajar kudi a kasar Sin. Cewa ya yi, kasar Sin ta samu karuwar farashin kaya a 'yan kwanakin baya ne sakamakon hauhawar farashin kayayyakin gona musammman ma kayan abinci. Saboda haka ne, babu yiwuwar ci gaba da samun hauhawar farashin kayayyaki daga dukkan fannoni. Mr. Zhu ya yi alkawarin cewa: " Gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar da manufar kudi kamar yadda ya kamata yayin da take mayar da kayyade karuwar farashin kaya a matsayin muhimmin aikinta na farko da zummar kyautata harkokin bunkasa tattalin arziki daga dukkan fannoni".

A karshe dai, Mr. Zhu ya bada karin haske cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara mai da hankali kan babban gibin dake tsakanin mazauna birane da kauyukan kasar a fannin samun kudin shiga, da ci gaba da nuna goyon baya ga sha'anin noma, da kauyuka da kuma manoma, da kara zuba makudan kudade ga yankunan dake yammacin kasar, da kafa wani cikakken tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta na birane da garuruwan kasar da kuma kara karfin karbar haraji da ake bugawa a kan kudin shiga na jama'a don daidaita yawan kudin shiga da ake samu tsakanin jama'ar kasar. ( Sani Wang )


1 2 3