Game da wannan tambaya dai, Mr. Zhu Zhixin ya bada amsa cewa: " Yanzu kasar Sin ba ta samun bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima a dukkan fannoni domin har wa yau dai ba a sauya dangantakar daidaito tsakanin samarwa da bukatu ba. Saboda haka, ba a samu karuwar farashi sosai ba a kasuwannin sayar da kwal, da wutar lantarki da mai da kuma kayayyakin sufuri da dai sauran makamantansu."
Sa'anan Mr. Zhu Zhixin ya bayyana cewa, ko da yake ba a samu saurin bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima ba a nan kasar Sin, amma ya kasance akwai sabani mai tsanani lokacin da ake gudanar da harkokin tattalin arziki. Gwamnatin kasar Sin ta lashi takobin daidaita wadannan matsaloli .
1 2 3
|