An labarta cewa, jiya Alhamis, a nan birnin Beijing, mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Mr. Zhu Zhixin ya fadi cewa, yanzu kasar Sin ba ta samun bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima a dukkan fannoni, wato ke nan ana samun daidaito tsakanin samarwa da bukatu a nan kasar, inda babu kasancewar karuwar farashi sosai a dukkan fannoni duk da cewa abubuwan da ake bukata sun fi yawa bisa wadanda ake samarwa.
Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin takan yi zamanta na duk kasa sau daya cikin shekaru biyar-biyar. Alkaluman da aka yi na nuna cewa, kasar Sin na rinka samun karuwar tattalin arziki sama da kashi 10 ko fiye cikin kashi 100 a kowace shekara tun bayan babban taron wakilan duk kasa na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka guanar a shekarar 2002, wato ke nan yawan karuwar tattalin arzikin ya ninka na sauran kasashen duniya sau biyu bisa na makamancin lokaci. Yanzu, wasu mutane sun bayyana shekkunsu cewa ko saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zai haddasa raguwar darajar kudi ?
1 2 3
|