Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 14:46:00    
An sake yin rantsuwar yaki da kangin talauci a duk duniya

cri

Wani muhimmin makasudin da aka tanada cikin manufar samun bunkasuwa ta shekaru 1,000 ta M.D.D. cewa, zuwa shekarar 2015, za a rage rabin yawan mutane masu talauci. Mr. Ban ki-moon ya yi bayyani kan wannan batu cewa, bisa ci gaban da ake samu a halin yanzu an ce, za a iya tabbatar da wannan manufa a wancan lokaci. Amma ci gaban da aka samu a duk duniya bai zama daya ba, har ila yau ana fuskantar kalubale masu tsanani a wasu bangarori, tun ba shiyyoyin da ke kudancin Sahara na Afirka ba. Sabo da haka ya yi kira ga kasashen duniya cewa, dole ne su mai da hankali kuma su yi amfani da albarkatun kasa musamman domin bunkasa shiyyoyi marasa ci gaba da mutane masu talauci.

Yayin da Mr. Rachel Miahnja, wakilin jami'an M.D.D. yake yin jawabi bisa sunan Sha Zukang, mataimakin babban sakataren kula da harkokin tattalin arziki da zaman al'umma na majalisar, ya bayyana cewa, "Aikin da ke gabanmu yana da wuya kwarai, ko da yake yanzu muna matukar kokari, amma har ila yau da akwai mutun daya daga cikin kowadanne mutane 5 wadanda suke yin fadi-tashi domin zaman rayuwarsu."(Umaru)


1 2 3