A gun bikin da aka yi a hedkwatar M.D.D., babban sakatare Ban Ki-moon na majalisar ya yi gajeren jawabi cewa, "A yayin zuwan zagayuwar ranar duniya ta 20 ta rage talauci, bari mu tashi tsaye, mu kaddamar da manufar siyasa, kuma mu yi kokari domin kawar da talaucin dan adam kwata-kwata."
Cikin jawabin da Mr. Ban Ki-moon ya yi, kuma ya bayyana cewa, bayan da aka shiga cikin wani sabon lokaci na shekaru dubu daya, shugabannin duk duniya baki daya sun lashe takobi ga masu talauci na duk duniya cewa, ya kamata a samu tabbaci ga kowane yaro don ya gama karatu daga makarantar firamare, kuma kowane mutun zai samu ruwan sha mai inganci, kowane iyali zai iya kubutar da kansa daga shure-shuren mutuwa sabo da munanan cututtuka ciki har da zazzabin malariya, haka ma ya kamata a kafa wata duniya wadda ta rage yawan gurbatacciyar iskar da ke dumama yanayi ta hanyar yin kokari tare tsakanin kasashe daban-daban. Abu mafi muhimmanci shi ne, ya kamata shugabanninmu su kafa wata duniya wadda a ciki ba wanda ke yin shure-shuren kangin talauci sosai.
1 2 3
|