Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 14:46:00    
An sake yin rantsuwar yaki da kangin talauci a duk duniya

cri

Ran 17 zuwa ran 10 ga watan Oktoba rana duniya ce ta rage talauci, a wannan rana da yamma an yi bikin tunawa da wannan rana a hedkwatar M.D.D. da ke birnin New York na kasar Amurka. To, kanun bayanin shi ne "An sake yin rantsuwar yaki da kangin talauci a duk duniya".

Kidan da kuke saurara yanzu ya zo ne daga 'yan fasaha na kasar New Zealand wadanda suka yi a gun bikin tunawa da ranar duniya ta rage talauci da aka yi a filin ciyayi da ke arewacin hedkwatar M.D.D. Cikin amon kide-kiden da aka yi, babban sakatare Ban Ki-moon na majalisar yana daukar hoto tare da wakilan mutanen kasashe daban-daban wadanda suka zo don halartar bikin, daga cikin su kuma da akwai mutane da yawa da suka zo daga kasashe mafiya talauci na duniya.

Shekarar nan shekara ce ta cikon shekaru 20 da aka fara yin kamfen din yaki da talauci a duk duniya. A ran 17 ga watan Oktoba na kafin shekaru 20 da suka wuce, dubban mutane sun taru a birnin Paris, hedkwatar kasar Faransa, inda suka yi rantsuwar yaki da kangin talauci. A yau wato ran 17 ga wata a hedkwatar M.D.D. kuma a birane da yawa na wasu kasashe, wata kungiyar yin yaki da talauci wadda take kunshe da babban sakataren M.D.D. da wakilan kasashe mambobinta daban-daban, da shugabanni da kuma mutane masu talauci na kasashe daban-daban wadda kuma ta sake yin rantsuwar yaki da kangin talauci.


1 2 3