A cikin jawabin da shugaban kasar Jamus ya yi ya bayyana cewa, wajen yin fama da jin 'yunwa, muhimmin aiki shi ne ba da tabbaci ga mutane da za su iya kokarin samun isasshen abinci a gonakinsu ko a shiyyar da ke kusa da wurinsu, saboda haka ana bukatar kafa wani ikon mallaka a kasashe masu tasowa don tafiyar da aikin noma yadda ya kamata. Amma abin bakin ciki shi ne, a kasashen da ke kudu, an raya aikin noma ta rikitacciyar hanya, kuskure mai tsanani shi ne kuskuren da aka maimaita shi.
bisa kimantawar da kungiyar abinci da noma ta yi, an ce, a duk duniya, da akwai mutane da yawansu ya kai miliyan 840 da suke fama da jin 'yunwa a shekara da shekaru, daga cikinsu, yawan mutanen kasashe da jihohi masu tasowa ya kai miliyan 800, yawancinsu suna Afrika. Game da wannan, shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Mrisho ya bayyana cewa, yanzu, a duk duniya, da akwai yaran da yawansu ya kai dubu 4 da suka mutu bisa sanadiyar fama da rashin abubuwa masu gina jiki da kamuwar ciwace-ciwace. Su ne mutanen da aka kwace musu ikon samun abinci.(Halima) 1 2 3
|