Ranar 16 ga watan Oktoba ranar abinci ce ta duniya ta Majalisar Dinkin Duniya. A wannan rana, a birnin Roma, babbar hedkwatarta, kungiyar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya bikin tunawa da ranar abincin duniya ta 27. Babban jami'in kungiyar Mr Jacques Diouf da shugaban kasar Jamus Mr Horst Koehler da shugaban kasar Tanzaniya Mr Jakaya Mrisho da sauran manya sun halarci bikin na taya murna, kuma sun bayar da jawabai, inda suka karfafa cewa, ikon bunkasa abinci shi ne babban hakkin dan Adam .
An kafa kungiyar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 1945, kuma tana daya daga cikin manyan hukumomin musamman na Majalisar Dinkin Duniya. Babbar dawainiyarta ita ce samar da wata duniya da ke iya samun ingancin abinci. A shekaru 70 na karnin da ya gabata, bisa sharadin da aka samu na samun rikicin abinci a duk duniya, babban taro na 20 da kungiyar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta kira a shekarar 1979 ya tsai da cewa, an mayar da ranar da aka kafa kungiyar bisa matsayin ranar abincin duniya don yi wa gamayyar kasa da kasa kaimi wajen mai da muhimmaci sosai kan aikin noma da ingancin abinci. Shekarar da muke ciki ranar abincin duniya ce ta 27 , babban jigonta shi ne hakkin abinci, wanda ya bayyana cewa, a kowace rana, gamayyar kasa da kasa suna kara fahimtar amfanin hakkin dan Adam da ke kara muhimmancin taimako ga yaki da talauci da jin 'yunwa. A gun bikin budewar taron murnar ranar, babban jami'in kungiyar abinci da noma Mr Jacques Diouf ya bayar da jawabin da ke da babban batu cewa, muhimmancin daukar matakai domin tabbatar da ikon samun abinci . Ya bayyana cewa, don kafa wata duniya cikin daidaito, babban jigon ranar abincin duniya na shekarar da muke ciki shi ne imuhimmancin tabbatar da kon bunkasa abinci. Abincin da aka fitar da su a duniya ya iya biyan bukatun dukkan mutanen duniya wajen yawansu da ingancinsu. Amma, a yau da dare, ana ci gaba da samun maza da mata da yara da yawansu ya kai miliyan 854 da suka shiga barci a yayin da suke fama da jin 'yunwa. Saboda haka ya kamata mu mai da muhimmanci ga mutane wajen dora hankulanmu da tsara manufofinmu da aiwatar da ayyukanmu.
1 2 3
|