Tun daga shekarar 1996 da aka kira taron shugabanni dangane da abincin duniya har zuwa yanzu, kungiyar abinci da noma da gwamnatocin kasashe daban daban na duniya suna kokari sosai cikin hadin guiwa don neman ikon samun abinci. Saboda haka babban ikon ya sami amincewa. Yanzu da akwai kasashe 156 da suka tabbatar da yarjejeniyar duniya dangane da ikon tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adu, kuma sun amince cewa, ikon samun abinci shi ne dawainiyar sa kai da ke da karfin shari'a. A cikin nasa jawabi, Mr Diouf ya karfafa cewa, ba da tabbaci da kowane mutum da zai iya samun isasshen abinci a yau da kullum ba ma wata bukata ce kawai wajen mutane ba, hatta ma jari ne da aka zuba don samun babbar fa'ida daga tattalin arziki, wannan wani babban iko ne da ba a iya kwace shi a fannoni da yawa. Duniya tana da hanyar da za a bi don cim ma ikon samun abinci, saboda haka lokacin ya yi da ake yin aiki a kai.
1 2 3
|