
"bayan da na ba shi kwas din horaswa, sannu a hankali kare ya iya tafiya, ya iya zauna, kuma ya iya kwance a kirjinsa. Daga baya kuma ya iya ja gora ga makafi wajen ketare hanya, ganin haka ko da yake na sha aiki sosai, amma na yi farin ciki kwarai da gaske."
A watan Mayu na shekarar da muke ciki, karnuka biyu masu ja gora da suka zo daga sansanin horar da kare dan ja gora na birnin Dalian sun shiga wadannan harkokin gasa ta 7 ta wasannin nakasassu na duk fadin kasar Sin. Hui Liangyu, mataimakin firayim ministan kasar da ya halarci gasar ya bayyana cewa, dole ne kasar Sin ta ba da tabbaci ga bunkasuwar aikin karnuka 'yan ja gora a fannonin dokoki da muhallin zaman al'umma. Sabo da haka ana yin imanin cewa, tabbas ne aikin horar da karnuka mai ja gora na kasar Sin zai samu bunkasuwa sosai bisa goyon bayan gwamnati da kuma kulawar zaman al'umma.
To, jama'a masu sauraro, karshen shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka Kande nake cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao) 1 2 3
|