Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 14:58:34    
Kasar Sin tana raya aikin horar da karnuka 'yan ja gora domin ba da hidima ga makafi

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke jan akalar shirin. A wadannan shekaru 2 da suka gabata, ana ta bunkasa aikin horar da karnuka 'yan ja gora a kasar Sin domin ba da sauki ga makafi wajen zaman rayuwarsu. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani a kan batun.

Kasar Sin wata kasa ce da ke da mutane mafi yawa a duk duniya, haka kuma ita kasa ce da ke da makafi mafi yawa a duniya, wadanda yawansu ya kai fiye da miliyan 12. Makafi su kan sha wahaloli sosai wajen zaman rayuwa, amma bisa matsayinsu na abokan arzikinsu, karnuka 'yan ja gora suna iya tallafa musu wajen yin zaman rayuwa kamar yadda ya kamata.

A kan wani titin kasuwa na birnin Dalian na lardin Liaoning da ke arewacin kasar Sin, ana iya ganin wata makauniya da wani karen Labrador Retriever a ko wace rana, suna farin ciki suna tafiya. Sunan wannan mace shi ne Zhang Shujun, ita da kuma mijinta dukkansu makafi ne. Sabo da ba ta iya ganin duniya, shi ya sa a cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, ko kusa ba ta yi mu'amala tare da waje ba. Yau da rabin shekarar da ta gabata, kare dan ja gora wanda ake kiransa Maomao ya zo gidanta, sabo da haka kullum ana iya sauraron muryar murna a cikin wannan gida.

Zhang Junshu ya gaya wa wakilinmu cewa, ba da jimawa ba, ita kadai da kare dan ja gora sun koma garinta cikin jirgin kasa, wanda ya kai kilomita daruruka da ke nesa da birnin Dalian, ta haka ta cimma burinta na sake saduwa da iyalanta. Kuma ta kara da cewa, "ina ganin cewa, bisa taimakon da karen ya ba ni, babu bambanci da ke tsakanina da sauran mutane, sabo da haka na yi imani sosai da zaman rayuwa. Yanzu na iya yin dukkan abubuwan da nake so, karen ya saukaka mini al'amura sosai."

Maomao, kare dan ja gora da ya iya warware matsalolin zaman rayuwa ga Zhang Shujun ya zo daga sansanin horar da karnuka 'yan ja gora na jami'ar koyon ilmin likitanci ta birnin Dalian, wannan shi ne sansani daya tak na babban yankin kasar Sin wajen horar da karnuka 'yan ja gora. Dr.Wang Jingyu, shugaban sansanin ya gaya mana cewa, yanzu akwai makarantu fiye da 80 na horar da karnuka 'yan ja gora a kasashe 27, kuma karnuka 'yan ja gora fiye da dubu 20 na duk duniya suna gudanar da aikin ba da hidima ga makafi. Yawan makafi na kasar Sin ya kai fiye da miliyan 12, shi ya sa kasar Sin tana bukatar horar da dimbin karnuka 'yan ja gora.

1 2 3