Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 14:52:52    
Mutanen da su kan ci kayayyakin kwalama da yawa sun fi sauki samun kiba fiye da kima

cri

A cikin wannan bincike da aka yi har shekaru 10 ga matasa fiye da 3000, Barry Austin, wani manazarci na jami'ar North Carolina ta kasar Amurka da abokan aikinsa sun gano cewa, bisa dakunan cin abinci na gargajiya, mutanen da su kan ci abincin a cikin dakunan sayar da kayayyakin kwalama sun fi saukin samun karuwar jimlar BMI, wanda wani ma'aunin nauyin jiki ne da a kan yi amfani da shi a duk duniya domin auna ko wani yana da jiki sosai, ko wani yana da kiba. Amma yaya aka iya samun wannan jimla? Alal misali, idan nauyin jikin wani mutum ya kai kilogram 80, kuma tsayinsa ya kai mita 1.85, to 80 a raba da 1.85 sau 1.85 shi ne 23.3 wato jimlarsa ta BMI. Idan wannan jimla ta kai 20 zuwa 25, wannan ya shaida cewa wannan mutum yana da koshin lafiya. Idan wannan jimla ta kai 25 zuwa 30, to wannan mutum ya samu kiba kadan, amma idan wannan jimla ta zarce 30, to wannan ya shaida cewa wannan mutum ya samu kiba fiye da kima.

Kididdigar da manazarta suka samu bayan shekaru 7 da suka gudanar da wannan bincike ta bayyana cewa, idan an ci kayan kwalama sau daya a ko wane mako, to jimlarsa ta BMI za ta karu da 0.13 a cikin wannan shekara, wannan ya yi daidai da karuwa da kilogram 0.42 ga wani mutumin da tsayinsa ya kai mita 1.78. Haka kuma kididdigar da suka samu bayan shekaru 10 da suka gudanar da binciken ta bayyana cewa, idan an ci kayan kwalama sau daya a ko wane mako, to jimlarsa ta BMI za ta karu da 0.24.

Idan An samu kiba fiye da kima, to hadarin kamuwa da cututtuka zai karu. Cibiyar nazari kan kiwon lafiya ta kasar Amurka ta bayar da wani rahoton cewa, idan wani mutum ya samu kiba fiye da kima, to hadarin kamuwa da sankarar hanji zai karu.


1 2 3