Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 09:13:07    
Shanghai ta kara mayar da mutane a gaban kome bisa taron wasannin Olympic na musamman

cri

Don kara fahimtar juna da zumunci a tsakaninsu da 'yan wasan Olympic na musamman na kasashe daban daban, da hannu biyu biyu ne unguwanni 144 da kuma iyalai 1877 na Shanghai suka karbi 'yan wasan Olympic na musamman na wurare daban daban na duniya da su zama da kuma kai ziyara.

Shanghai ta kawatar da dimbin 'yan wasan Olympic na musamman da malaman horas da wanni da suka zo kasar Sin a karo na farko sosai. Kulawar da mazaunan Shanghai ke nuna wa 'yan wasan Olympic na musamman ta burge malama Diamond Green, wata malamar horas da wasanni ta kungiyar kasar Amurka, ta ce,'Kowa da kowa na da kirki, suna nuna ladabi yadda ya kamata, suna maraba da mu da hannu biyu biyu. Mun ji farin ciki saboda zama a iyalin mazaunin Shanghai. A sa'i daya kuma, 'yan wasan Olympic na musamma sun ji farin ciki sosai saboda sun sami sabbin abokai a wajen, sun kuma kara fahimtarsu kan al'adu daban daban.'

Ana mai da hankali kan rukuni maras karfi, kamar su nakasassu a kwakwalwa, da kuma kula da su yadda ya kamata bisa tunanin mayar da mutane a gaban kome. Irin wannan tunani kuwa ya zama abin tilas wajen raya birni har ma duk kasa mai jituwa. Shahararren dan wasan kwallon kwando Yao Ming na kasar Sin ya yi shekaru 3 yana aikin jin kai na taron wasannin Olympic na musamman. Ya gano dimbin sauye-sauye saboda shirya taron wasannin Olympic na musamman a garinsa. Ya ce,'A ganina, sauye-sauyen da muka samu a shekarun baya da suka wuce shi ne kara fahimtarmu kan wadannan mutane na musamman. Ga misali, na ji an ce, sun zama a iyalan fararen hula a wannan karo, sun yi zaman cude-ni-in-cude-ka tare da saura. Wannan ya kara samar mana damar kara fahimtar juna. Ina tsammani cewa, hakan ya ba su taimako a nan gaba.'


1 2 3