Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 09:13:07    
Shanghai ta kara mayar da mutane a gaban kome bisa taron wasannin Olympic na musamman

cri

A makon jiya, an rufe taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na duniya na shekarar 2007 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Wannan ne karo na farko da aka shirya taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na duniya a wata kasa mai tasowa, a kasar Asiya, a kasar Sin. A cikin irin wannan gagarumin taron wasammin motsa jiki na duniya, nakasassu a kwakwalwa fiye da dubu 10 na gida da waje sun zama taurari a kan dandamalin duniya, a Shanghai. Shanghai kuwa, wadda ta shahara bisa nasarorin bunkasuwar tattalin arziki, tana samar wa nakasassu a kwakwalwa na duk duniya kauna da kuma fata. Haka kuma, kasar Sin mai ji da kai, wadda ke bude kofarta ga duniya, tana nuna wa kasashen duniya sakamakon da ta samu a fannin bunkasa sha'anin hakkin dan Adam.

A 'yan kwanankin nan da suka wuce, a ko ina a Shanghai, an iya ganin hotunan 'yan wasan Olympic na musamman. Shanghai ta taba bakuncin manyan gasannin duniya da yawa, amma shirya taron wasannin Olympic na musamman ya jarraba mata a fanninin sharuddan na'urori da kuma karfin shirya gasa, sa'an nan kuma, ya gwaje kaunar da mazaunan birnin ke nunawa. Tunani na samun sauye-sauye, mutane na nuna budaddiyar zuciya, haka kuma, suna son nuna wa saura kauna. Sakamakon karamin bincike da aka yi ya nuna cewa, mazaunan Shanghai kimanin kashi 92 cikin kashi dari sun san taron wasannin Olympic na musamman. Malama Liu Huilan, 'yar birnin Shanghai, ta gaya mana cewa,'An yi taron wasannin Olympic na musamman a birninmu Shanghai, a idon dukkan mazaunan birninmu, wannan ya yi kyau kwarai. A lokacin hutu, abokaina da ni mun je dakunan wasa don kallon gasa, mun karfafa gwiwar 'yan wasan Olympic na musamman. Mun gano cewa, kula da rukuni maras karfi wani babban nauyi ne da aka danka mana.'


1 2 3