Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-16 19:14:17    
Jama'ar kasar Sin suna mai da hankulansu a kan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin

cri

A hakika dai, a gidan Ni Juan, ba ma kawai Ni Juan tana mai da hankali a kan batun samun aikin yi ba, har mahaifinta Ni Yangang shi ma yana sa lura sosai a kan matakan da gwamnati za ta dauka a kan batun. Da ma shi wani ma'aikaci ne na wani kamfani mallakar gwamnati, bayan da aka sallame shi daga aikinsa a shekaru fiye da 10 da suka wuce, sai ya fara aikin sayar da kayayyaki. Amma bisa karuwar shekarunsa da haihuwa, sai ya fara damuwa kan ko za a sake sallamarsa daga aiki."Idan shekarunka ya wuce 50 da haihuwa, watakila aikin da kake yi ba zai ci gaba da dacewa da kai, shi ya sa mai yiwuwa ne za a sake sallamarka daga aiki, kuma da wuya ne ka sake samun aikin yi. Ina ganin ya kamata gwamnati ta dora muhimmanci a kan batun, kuma ta yi kokarin tabbatar da zaman rayuwar mutanen da ke fama da matsalar."

A nan kasar Sin, kamar yadda iyalan Ni ke yi, kusan kowa na mai da hankalinsa a kan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin. Sabo da jama'a na son gano ra'ayoyin jam'iyyar da ke jan ragamar mulki a fannin tafiyar da harkokin kasa, kuma su ga irin tasirin da za a kawo wa zaman rayuwarsu. Rahoton shugaba Hu Jintao ya faranta ran jama'a, sabo da sau tari ne rahoton ya ambaci batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama'a.

Wakilai mahalartan taron su ma sun gano batun. Mr.Song Xuantao, wani wakili daga birnin Zhumadian na lardin Henan na kasar Sin, ya bayyana cewa,"jam'iyyarmu da kuma gwamnati suna dora batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama'a a wani muhimmin matsayi, don kara amfana wa jama'a da kuma kawo musu alheri. Wannan ya bayyana manufar jam'iyyar kwaminis ta Sin ta gudanar da mulki domin jama'a da kuma mayar da harkokin jama'a a gaban kome."(Lubabatu)


1 2 3