A gun bikin bude taron, a madadin tsohon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ne, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar, ya gabatar da rahoton aiki, kuma nasarorin da Sin ta cimma tun bayan da ta aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da Mr.Hu Jintao ya bayyana cikin jawabinsa, sun burge Madam Du Wenfang sosai. Ta ce,"A shekarar 1974, albashina ya kai kudin Sin yuan 40 ne kawai a cikin ko wane wata. Bayan da Sin ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare da kuma bude kofa ga kasashen waje, sai albashina ya yi ta karuwa shekara da shekaru. Yanzu na iya samun kudin fansho da yawansa ya wuce yuan dubu a ko wane wata. Ka ga yadda zaman rayuwar jama'a ya sami kyautatuwa."
Ni Juan jika ce ta Madam Du Wenfang, kuma tana karatu a jami'ar koyon ilmin tattalin arziki da ciniki ta birnin Beijing. A ran nan, bayan darasi, Ni Juan ta karanta rahoton Hu Jintao daga internet, kuma ta gano cewa, rahoton ya ambaci batun samar da guraben aikin yi ga dalibai wanda ke daukar hankalinta sosai. Ta ce,"yanzu da kyar dalibai ke samun aikin yi bayan da suka gama karatu. Daga rahoton, muna iya gano cewa, gwamnati ma ta gano matsalar, har ma rahoton ya gabatar da kyautata aikin samar da guraben aikin yi ga dalibai."
1 2 3
|