Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-16 12:23:27    
Kasar Sin na goyon bayan karfafa karfin Afirka ta fuskar ciniki ta hanyar ba da tallafi

cri

A karshe dai, ya gabatar da shawara ga babban taron cewar, ya kamata kasashe masu sukuni da ke fi cin gajiya daga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da kuma yin ciniki a tsakanin kasashen duniya cikin 'yancin kai su kara daukar nauyi bisa wuyansu, suna da alhakin kara bai wa kasashe masu tasowa taimako. Haka kuma kamata ya yi kungiyar WTO da Bankin kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin harkokin tattalin arziki na kasa da kasa su taka rawarsu ta ba da tallafawa a tsakanin bangarori daban daban cikin himma da kwazo.

Dadin dadawa kuma, wakilan bangarorin ba da taimako da suka hada da kasashen Amurka da Japan da Norway da Kungiyar Tarayyar Turai wato EU da hukumar yin hadin gwiwa da bunkasa tattalin arziki wato OECD da Bankin kasa da kasa sun kuma bayar da jawabi a gun wannan muhimmin babban taro.

A lokacin da kungiyar WTO ta shirya taron ministoci a yankin musamman na Hong kong na kasar Sina watan Disamba na shekarar 2005, ta gabatar da tsarin ba da taimakon ciniki, za ta kuma soma gudanar da tsarin a watan Oktoba na shekarar da ta gabata. Kungiyar WTO ta taba shirya babban taron ciniki na ba da taimako ga kasashen Asiya da tekun Pacific da kasashen Latin Amurka a watan Satumba na shekarar da muke ciki. Kungiyar WTO da kwmaitin kula da tattalin arzikin kasashen Afirka na Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Raya Afirka su ne suka shirya wannan babban taron ciniki na ba da tallafi ga kasashen Afirka cikin hadin gwiwa. Bugu da kari kuma, kungiyar WTO za ta yi kimantawa kan wannan manyan taruruka 3 a watan Nuwamba na wannan shekara, za ta kuma tsara matakan ba da taimako a tsakanin bangarori daban daban da kuma a tsakanin bangarori 2 domin sa kaimi kan kasashe masu tasowa da su karfafa karfinsu na yin cinikin duniya.(Tasallah)


1 2 3